Wani sanatan Amurka ya soki nasarar Paul Biya

0
1000250481
Spread the love

Shugaban kwamitin majalisar dattawan Amurka kan dangantakar ƙasar da ƙasashen waje, Sanata Jim Risch ya bayyana sake zaɓen Paul Biya a matsayin abin kunya.

Matakin ɗan majalisar dattawan na zuwa ne a daidai lokacin da jagoran adawar ƙasar, Issa Tchiroma Bakary ke ci gaba da iƙirarin nasara.

A cikin jerin saƙonnin da ya wallafa a shafinsa na X, Mista Risch ya zargi gwamnatin Biya da abubuwa da dama, da suka haɗa ”far wa ƴan’adawa, da tsare Amurkawa ba bisa ƙa’ida.

Haka ma ɗan’majalisar a Amurka ya zargi gwamnatin Biya da bai wa sojojin hayar Rasha na Wagner damar gudanar da abin da ya kira ”miyagun” ayyuka da kuma samar da wani yanayi da ya bai wa Boko Haram da ISIS damar gudanar da ayyukansu.

“Kamaru da ƙawar Amurka ba ce, hasalima tana haifar da barazanar tattalin arziki da tsaron Amurkawa,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa ”lokaci ya yi da ya kamata a sake nazarin dangantakar ƙasashen biyu kafin lamarin ya yi ƙamari.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *