Jam’iyyar APC ta kai karar hadimin Binani kotu a kan rubutun sa a shafin Facebook.

Gungun ‘yan majalisar zartaswar jam’iyyar APC reshen karamar hukumar Gombi ta jihar Adamawa, ta shigar da karar Adamu Ibraheem Jimeta, mai taimaka wa ‘yan takarar gwamna a jam’iyyar a zaben 2023, Sanata Aishatu Ahmed, wacce aka fi sani da Binani.
A kwanakin baya ne Binani ta sauya sheka zuwa jam’iyyar (ADC) daga jam’iyyar APC.
Sai dai karar da aka shigar a Kotun Koli ta Upper Area mai lamba 1 da ke Yola, mai lamba UACY/CR/68/2025, ta ce Jimeta ya wallafa abubuwan batanci a shafinsa na Facebook a ranar 24 ga Yuli, 2025.

A cewar karar, sanarwar ta yi ikirarin cewa wasu jami’an jam’iyyar APC daga karamar hukumar Gombi ta jihar sun fice daga jam’iyyar.
An yi zargin cewa takardar ta lissafo sunayen wadanda suka yi korafin, ciki har da na wata matacciyar ‘yar jam’iyyar, Ishiya Jannatu.
Jami’an jam’iyyar APC 13 da suka hada da Abdulsalam Usman, Yohanna Peter, Mohammed Garba Nyako, da Christiana Livingstone, sun bayyana cewa labarin ba gaskiya bane kuma ya 6ata musu suna.
A cikin korafin da suka yi na rantsuwar, jami’an sun bayyana cewa, rubutun nasa ya haifar da rudani a cikin jam’iyyar, domin wasu jiga-jigan jam’iyyar APC sun yi kira da a dakatar da su ko kuma a tsige su gaba daya.
Masu korafin sun kara da cewa an yi kokari da dama don ganin Jimeta ya janye rubutun nasa tare da bayar da bayani, amma ya ki amincewa.
Sai dai, duk da haka, ya goge sakon bayan wani lokaci kadan.Masu korafin sun roki kotun da ta yi bincike kan laifuffukan da suka shafi bata suna, sabanin sashe na 377 da 318 na dokar laifuka ta jihar Adamawa ta shekarar 2018.
Sun kuma bukaci kotun da ta yi shari’ar ta hukunta wanda ake kara a karkashin sashe na 378 da na 319 na wannan doka.
An tsayar da ranar 4 ga watan Agusta domin sauraren karar, amma duk kokarin jin ta bakin Sanata Binani ko wanda ake kara ya ci tura.
