WAFCON: An bukaci hukumar kwallon kafan Africa CAF da ta dauki mataki kan halayyan da magoya bayan Morocco suka nuna.

Ana ci gaba da nuna damuwa kan yadda aka kaiwa ‘yan wasa hari a lokuta daban-daban na gasar kwallon kafan mata na Hukumar Kwallon Kafa ta Afirka (CAF) da aka kammala a baya-bayan nan, musamman wanda aka kai wa ‘yan wasan Super Falcons ta Najeriya hari a wasan karshe na gasar cin kofin Afirka ta mata na 2025 (WAFCON) da suka yi da Morocco a karshen mako.
Idan ba’a manta ba Super Falcons ta lallasa Morocco da ci 3-2, inda suka daga kofin na WAFCON karo na 10.
Amma a yayin karawar da suka yi a filin wasa na Olympique de Rabat, an ga fitulun Laser a fuskokin ‘yan wasan Super Falcons kamar Esther Okoronkwo da Michelle Alozie don dauke musu ido daga filin wasan da hanyar disashe ganin su musamman a lokacin bugun fanariti, bugun daga kai sai mai tsaron gida.
Magoya bayan Morocco sun yi amfani da fitilun Laser azaman dabara don karkatar da abokan adawar.
Da yake jawabi bayan da Najeriya ta doke Morocco, babban kocin Super Falcons, Justin Madugu, ya bayyana bakin cikinsa kan yadda magoya bayan Morocco suka yi amfani da hasken Laser a kan ‘yan wasansa.
