Waɗanda suka rasu a fashewar tankar mai a Neja sun ƙaru zuwa 45

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya NEMA ta ce adadin waɗanda suka rasu a sanadiyar fashewar tankar man fetur a babban titin Bida zuwa Agaie a ƙaramar hukumar Katcha na jihar Neja sun ƙaru zuwa 45.
Hukumar ta ƙara da cewa zuwa yanzu akwai kusan mutum 63 da suke ci gaba da jinyar raunukan da suka samu, kamar yadda babban jam’in hukumar na shiryar jihohin Kwara da Neja ya bayyana wa tashar Channels a ranar Juma’a.
“Mun tabbatar da mutuwar mutum 45, maza 12 mata 27, sannan a akwai ƙananan yara guda shida.
A ɓangaren waɗanda suka jikkata kuwa akwai kusan mutum 63, maza 24 mata 32 da ƙananan yara shida,” in ji shi.
