Venezuela za ta sayi kayayyakin Amurka da kuɗin man fetur ɗinta – Trump

Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce Venezuela ta amince ta yi amfani da kuɗin da za a samu daga sayar da manta, ta rinka sayen kayan da aka yi a Amurka kawai.
A wani sako da ya sanya a shafinsa na sada zumunta Trump ya ce, kayan da za ta rinka saya, za su haɗa da kayan gona, da magunguna, da kuma na’urori don inganta cibiyoyinta na samar da makamashi.
A halin da ake ciki kuma ministan harkokin cikin gida na Venezuelar, Diosdado Cabello, ya ce mutum 100 da suka haɗa da fararen hula, suka mutu a harin da Amurka ta kai ranar Asabar, lokacin da ta kama Shugaban ƙasar Nicolas Maduro, ta yi gaba da shi zuwa kasarta.
Ya ce matar Maduron, Cilia Flores ma ta ji rauni a kai a lokacin da sojojin ke kama ta.
