UNICEF ta cimma yarjejeniyar rage farashin allurar rigakafin malaria

Asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF, ya cimma yarjejeniya domin rage farashin allurar rigakafin cutar zazzabin cizon sauro wato malaria wadda zata ya kare yara maza da mata miliyan bakwai da ga cutar zuwa nan da shekarar 2030.
Farashin allurar rigakafin samfurin R21, wanda yanzu yake kan kudi dala hudu zai koma dala uku sakamakon yarjejeniyar da aka cimma da kamfanin daya samar da ita wato GAVI.
Kudin da aka ragen zai ba wa kasashe damar siyan adadi mai yawa.
Har yanzu cutar malaria na daya daga cikin cutukan da suke da mummunar illa a duniya inda Majalisar Dinkin Duniya ta ce yaro daya na mutuwa a kowanne minti daya sakamakon cutar.
