Trump ya faɗa wa ƴan Iran su ci gaba da zanga-zanga

0
1000443741
Spread the love

Shugaban Amurka Donald Trump ya faɗa wa al’ummar Iran cewa su jajirce sannan su ci gaba da zanga-zanga.

Trump ya faɗi haka ne a wani sako da ya wallafa a kafar sada zumunta na Truth Social.

“Ku ci gaba da zanga-zanga ƴan Iran – Ku mamaye hukumominku, ku rubuta sunayen waɗanda suke kisa da kuma aikata ɓarna. Za su ɗanɗana kuɗarsu.

“Na soke duk wata tattaunawa da jami’an Iran har sai an dakatar da kashe masu zanga-zanga.Taimako na nan zuwa,” in ji Trump.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *