Tinubu ya rantsar da Chris Musa ministan tsaron Najeriya

0
1000344423
Spread the love

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya rantsar da Janar Christopher Musa a matsayin ministan tsaron ƙasar bayan amincewar majalisar dattawa.

An yi bikin rantsar da tsohon babban hafsan tsaron ne a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja a yau Alhamis, kwana ɗaya bayan ‘yanmajalisar dattawan sun shafe kusan awa biyar suna yi masa tambayoyi yayin tantance shi.

Mai magana da yawun fadar shugaban ƙasa Bayo Onanuga ya wallafa hoton bikin rantsuwar a shafinsa na dandalin X.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *