Tinubu ya buƙaci majalisa ta gyara ƙundin mulki domin kafa ‘yansandan jihohi

0
1000372278
Spread the love

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya bukaci shugabannin Majalisar Dattawa su fara nazarin yiwuwar gyaran ƙundin tsarin mulki domin samar da dokar da za ta ba da damar kafa ‘yansandan jihohi, a wani yunkuri na magance matsalolin rashin tsaro da ke addabar ƙasar.

Shugaban ƙasar ya bayyana hakan ne yayin wata walimar buɗe baki da ya shirya wa sanatoci a fadar shugaban ƙasa, inda ya ce “lokaci ya yi da za a bai wa jihohi ƙarin iko wajen kula da tsaron yankunansu.

“Ya ce “kafa ‘yan sandan jihohi zai taimaka wajen daƙile ayyukan ta’addanci da garkuwa da mutane, da hare-haren ‘yan bindiga, tare da ƙarfafa tattara bayanan sirri da kuma saurin mayar da martani idan barazana ta taso a cikin al’umma.

“Tinubu ya jaddada cewa tsarin rarraba ikon ‘yan sanda zai taimaka wajen haɗa kai tsakanin hukumomin tsaro na tarayya da na jihohi, tare da inganta yadda ake gudanar da ayyukan tsaro bisa sahihan bayanai.

Ya kuma ce duk da kalubalen tsaro da ake fuskanta, gwamnati na da ƙudurin ganin an samar da mafita mai dorewa.

A nasa bangaren, shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya bayyana cewa sauye-sauyen da gwamnatin Tinubu ke aiwatarwa sun ƙara yawan kuɗaɗen shiga ga jihohi, abin da ya ce zai taimaka wajen samar da muhimman ababen more rayuwa da bunkasa ci gaba a fadin ƙasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *