Tinubu ya bayar da umarnin ɗaukar ƴansanda 30,000

Shugaban Najeriya ya bayar da umarnin a dauki yannanda 30,000 bayan sace-sacen mutanen da aka yi a kwanakin baya bayannan.
Ofishin Shugaban kasar Bola Tinubu, ya kuma sanar da cewa duk jami’an tsaron da ke kare manya masu fada aji a kasar a mayar da su sauran fagen daga domin su ji su ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin al’ummar kasar.
Wannan yunkurin ya zo ne bayan da yara 50 daga cikin fiye da 300 da aka sace a makarantar sakandire st Mary da ke jihar Neja suka kubuta daga hannun wadanda suka sace su.
Wakiliyar BBC ta ce an umarci makarantu a wasu sassan jihohin Najeriya da su rufe makarantun bayan sace sacen daliban da a ka yi a baya bayannan, sannan kuma bayan shafe mako guda a hannun masu satar mutane an sako mutum 38 da aka sace a wani coci a jiya Lahadi.
