Tarihi ba zai taɓa mantawa da Buhari ba – Bisi Akande

0
1000083252
Spread the love

Shugaban jam’iyyar APC na farko kuma tsohon gwamnan jihar Osun, Cif Bisi Akande ya jagoranci tawagar ƴansiyasa zuwa ta’aziyyar tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari.

Sun kai ziyarar ce gidan marigayin a jihar Kaduna ranar Laraba, inda Akande ya kwatanta shi da shugaba na gari wanda tarihi ba zai taɓa mantawa da shi ba saboda kyayawan ayyuka da ya yi a ƙasar.

Matar marigayin ne Aisha Buhari da kuma ɗansa Yusuf Buhari ne suka tarbi tawagar ƴansiyasar.

Akande ya nuna kaɗuwarsa kan mutuwar tsohon shugaban ƙasar, inda ya ce lokaci na karshe da suka haɗu shi ne lokacin da ya kai masa ziyara a Daura.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *