‘Suna saka hannun jari a cin hanci da rashawa’ – Peter Obi ya bayyana sirrin sayen kuri’u

Tsohon dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Labour, Peter Obi, ya bukaci ‘yan Najeriya da su guji sayen kuri’u, yana mai bayyana hakan a matsayin cin hanci da rashawa.
Obi ya ba da wannan gargaɗin a cikin wani rubutu a kan shafin sa na X ranar Litinin.
Tsohon Gwamnan jihar Anambra ya yi kira ga ‘yan kasar da su yi rajista, da kuma kiyaye katin zaben su na dindindin (PVCs), wanda ya bayyana a matsayin “gadar sabuwar Najeriya.”
Ya ce masu sayen kuri’u suna yin haka ne domin samun kudaden jama’a domin a wadata kansu.
Tsohon gwamnan jihar Anambra ya yi gargadin cewa sayar da kuri’u yana barazana ga samar da damammaki na ilimi, kiwon lafiya, da ayyukan yi a nan gaba.
Ya jaddada cewa dimokuradiyya za ta ci gaba ne kawai idan ’yan Najeriya suka dauki nauyi ta hanyar zaben shugabannin da ke da niyyan samarda sauyi nagari.
