Soludo ya rufe kasuwar Onitsha na mako ɗaya saboda ƙin bin dokar hana fita

Gwamnan jihar Anambra, Farfesa Chukwuma Soludo, ya umarci rufe Kasuwar Onitsha na tsawon mako guda, bayan ‘yan kasuwar sun ƙi bin dokar hana fita ta ranar Litinin.
Gwamnan ya bayar da wannan umarni ne a ranar Litinin yayin ziyarar sa a kasuwar tare da wasu daga cikin masu ba shi shawara da sauran jami’an gwamnati.
Soludo ya gargaɗi cewa idan ‘yan kasuwar sun ci gaba da ƙin bin umarnin, ana iya tsawaita rufe kasuwar, inda ya ƙara da cewa jami’an tsaro sun rufe kasuwar ne don aiwatar da dokar.
Soludo ya ce duk da tabbacin da aka bayar sau da yawa na inganta tsaro da kiran a farfaɗo da buɗe shaguna, ‘yan kasuwa da dama a wannan kasuwar sun zaɓi ci gaba da rufe shagunan su.
Soludo ya ce, “Gwamnati ba za ta tsaya tana kallo ba yayin da wasu ‘yan mutane ke ƙin bin dokoki ba, suna barazana ga lafiyar jama’a da watsi da umarnin gwamnati na dawo da zaman lafiya. Wannan cin zarafi ne na tattalin arziki.”
