Sojojin Najeriya sun mutu yayin samame a yankin Timbuktu

0
1000471524
Spread the love

Rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa wasu daga cikin dakarunta da na haɗin gwiwa ta JTF sun rasa rayukansu, yayin da wasu suka ji rauni a aikin samame da kuma ragargazar ƴanbindiga da sojojin ke yi a yankin Timbuktu.

Wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta ce a ranar 20 ga Janairun 2026, yayin da sojoji ke ƙoƙarin karɓe matsugunin ƴanbindigar a wani yankin tashar jiragen ruwa da ke kilomita 6 arewa da Chilaria, sun gamu da motoci biyu masu ɗauke da abubuwan fashewa.

Sojojin sun samu nasarar kawar da ɗaya daga cikin motocin, amma ɗayan motar ta fashe lamarin da ya yi sanadiyyar rasa rayukan wasu daga cikin dakarun da kuma raunata wasu.

An gaggauta ɗaukar waɗanda suka ji rauni zuwa asibiti domin samun kulawa.

Sanarwar ta kuma ce sojojin sun gano makeken kabarin ƴanbindiga da aka ƙiyasta yana ɗauke da gawarwaki guda 20 da aka kashe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *