Sojojin Najeriya sun kama mai ƙerawa Boko Haram jirage marasa matuƙa
Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta sun kama wasu mutane da ke aiki tare da Boko Haram da kuma wani mai samar da jirage marasa matuƙa yayin da suke ci gaba da daƙile ayyukan ‘yan ta’adda a jihohin Adamawa da Borno.
Cikin wani saƙo da rundunar sojin ta wallaf a shafinta na X, ta ce an samu nasarar kamen ne bisa haɗin kai masu gadi da mafarauta.
Sojojin sun ce a ranar Alhamis, sojojin sun kama Ismail Muhammed, mai shekaru 28, a yankin Visik na ƙaramar hukumar Hong, inda aka samu bindiga da sauran makamai da kayan soji da abinci iri-iri ttattare da shi.
Rundunar ta ce ta tsare shi a gidan yari domin ci gaba da bincike.
Sojojin sun kuma ce a wani aiki daban a ƙaramar hukumar Madagali, an hallaka Abdullahi Mafa, shugaban ‘yanbindiga, yayin da ake kai hari a layin Kogin Visik.
”Haka kuma, dakarun sun kama wani Dauda Usman Gubula, mai shekaru 64, wanda ke samar da jirage marasa matuƙa ga ‘yan ta’adda domin kai hare-hare kan sojoji”, in ji sanarwar.
Rundunar sojin ta ce dakarunta sun kuma daƙile wani hari da yanbindiga suka shirya kai wa a Ngamdu, Jihar Borno, sannan sun hallaka wani mai bayar da bayanan sirri ga ‘yan ta’adda da ke ƙoƙarin ƙetare shingen tsaro.
