Sojojin Najeriya sun kama ‘kayan haɗa bamabamai’ a jihar Yobe

0
1000170304
Spread the love

Rundunar sojan Najeriya ta ce ta yi nasarar kama motoci maƙare da kayayyakin da take zargi na harhaɗa bama-bamai ne da ake shirin tsallakwa da su Jamhuriyar Nijar.

A ranar 16 ga watan Satumba dakarun rundunar musamman ta Operation Hadi Kai ne suka kama wata babbar mota ɗauke da buhuhunan takin zamani 700 a kan hanyar Nguru zuwa Gashuwa na jihar Yobe.

“A wannan ranar ce binicke ya nuna cewa motar na ɗauke da buhun takin zamani 700, wanda ake haɗa bamabamai, da ƙwayoyi daban-daban, waɗanda aka ɓoye cikin kaya,” a cewar wata sanarwa da Kanal Sani Uba ya fitar.

“Bayanai sun nuna cewa an yi niyyar kai kayan ne Jamhuriyar Nijar, abin da ke nuna ayyukan safarar kayan ta’addanci tsakanin ƙasa da ƙasa.”

A cewarsa, sun kuma kama wata mota ɗauke da farantan samar da lantarki daga hasken rana da sauran kayayyaki, waɗanda bayanai suka nuna “‘yanta’adda na shirin tattara kayayyaki dinka wa mayaƙansu kakin soja ne”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *