Sojojin Najeriya sun daƙile harin mayaƙan ISWAP kan sansanin soji a Borno

0
1000367695
Spread the love

Dakarun sojin Najeriya a ƙarƙashin Operation HADIN KAI (OPHK) sun yi nasarar daƙile wani harin haɗin gwiwa da mayaƙan ƙungiyar ISWAP suka kai a wani sansanin sojoji da ke yankin Mairari na jihar Borno, inda suka yi mummunar illa ga ayyukan ƙungiyar a yankin.

Wata sanarwa da ta fito daga jami’in yaɗa labarai na na Operation Hadin kai Laftanar Kanar Sani Uba ta ce mayaƙan sun yi yunƙurin kutsawa sansanin ta hanyar amfani da abubuwa masu fashewa da aka ɗaura a jikn ababaen hawa.

Dakarun sun gano duka na’urorin nan da nan tare da kawar da su, tare da hana duk wani shiga cikin sansanin.

Hotunan faifan bidiyo da na CCTV sun tabbatar da cewa an kashe mayaƙan da dama, yayin da wasu suka samu munanan raunuka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *