Sojojin Madagascar sun ce sun karɓe mulkin ƙasar

0
1000220961
Spread the love

Rundunar sojin Madagascar ta ce ta karɓe mulkin ƙasar, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito.

Shi ma kamfanin dillancin labari na AFP ya ruwaito wani soja mai muƙamin Kanal na cewa sojoji sun karɓe mulki.

Kanal Michael Randrianirina, shugaban rundunar sojin da ke tsaron fadar shugaban ƙasar, ya karanta sanarwar karɓe mulkin a gidan radion ƙasar.

Yana mai cewa ”mun karɓe mulki daga yanzu”, kamar yadda ya karanta.

A ƙarshen mako ne rundunar da ke tsaron fadar shugaban ƙasar ta juya wa shugaban baya, ta hanyar shiga zanga-zangar masu neman ya sauka daga mulki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *