Sojoji sun yi gargaɗin samun ƙarin hare-hare a ƙarshen Ramadan
Major Janar Abdussalam Enesi Abubakar
Rundunar Operation HADIN KAI ta gargaɗi al’ummomi a arewa maso gabas kan yiwuwar samun ƙarin hare-haren kunar bakin wake daga Boko Haram da ISWAP a kwanakin ƙarshe na Ramadan, bayan fashe-fashen da suka auku a Maiduguri.
A cikin sanarwar da rundunar ta fitar a yau Talata 17 ga Maris 2026, ta ce irin waɗannan hare-hare na ƙaruwa ne a lokutan ibada, musamman a wuraren taruwar jama’a kamar masallatai da kasuwanni da kuma tashoshin mota.
Ta shawarci jama’a da su kasance cikin taka-tsantsan, su lura da abubuwan da ba su saba gani ba, su kuma bai wa jami’an tsaro cikakken haɗin kai.
Rundunar ta kuma tabbatar da cewa ta ƙara tsaurara matakan tsaro domin kare rayuka da dukiyoyi a fadin yankin.
