Sojoji sun kwato alburusai, kayayyaki bayan harin da jiragen ta suka kai a Banki

Dakarun Operation Hadin Kai sun kwato alburusai da sauran kayayyaki a wani samamen da suka kai a kusa da garin Banki da ke karamar hukumar Bama a jihar Borno.
Rundunar ta gudanar da aikin ne a ranar 19 ga watan Satumba tare da hadin gwiwar dakarun hadin gwiwa da Civilian Joint Task Force (CJTF), ta biyo bayan hare-haren da jiragen yakin ISWAP suka kai kwanan nan a harin da aka kai a Banki da Bula Yobe a ranar 18 ga watan Satumba wanda ya yi sanadin mutuwar ƴan ta’adan ISWAP akalla 32.
