Sojoji sun dakile jigilar makamai, sun kwato bindigogi a Kwara

0
1000184279
Spread the love

Dakarun na 22 Armored Brigade sun kashe wani mai jigilar makamai tare da gano tarin makamai a wani samame da suka kai a hanyar Share–Gbugbu a karamar hukumar Edu a jihar Kwara.

Wannan farmakin wanda aka gudanar a ranar Alhamis a karkashin rundunar Operation Park Strike V, ya biyo bayan sahihan bayanan sirri kan tashin makamai daga Birnin Gwari, jihar Kaduna.

Kakakin rundunar, Kaftin Stephen Nwankwo, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce sojojin sun tare wata mota kirar Volkswagen Golf 3 mai lamba Bayelsa SAG-133 XA da misalin karfe 8:30 na safe direban ya yi yunkurin tserewa amma sojojin suka dakile shi.

Binciken da aka yi wa motar ya kai ga gano bindigogin AK-47 guda biyar da kuma magazine guda uku da aka boye a cikin buhun gawayi.

Kwamandan, 22 Armored Brigade, Brig.-Gen. Ezra Barkins, ya yaba wa sojojin saboda taka-tsantsan da kwarewa, inda ya bukace su da su ci gaba da wannan aiki.

Ya kuma tabbatar wa mazauna jihar Kwara da makwafta cewa, rundunar zata ci gaba da jajircewa wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a, ya kuma yi kira da a kara hada kai da jama’a ta hanyar musayar bayanai masu inganci a kan lokaci.

A cewarsa, rundunar sojin Najeriya za ta ci gaba da yin aiki tukuru domin hana masu aikata laifuka ‘yancin gudanar da ayyukansu da kuma kawar da duk wani nau’in rashin tsaro a kasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *