Sojin Najeriya sun ce sun kashe jagoran ‘yanfashin daji a jihar Kogi

0
1000156281
Spread the love

Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta sun yi nasarar kashe jagoran ‘yanfashin daji Babangida Kachalla a jihar Kogi da ke tsakiyar ƙasar.

Gidan talabijin na Channels TV ya ruwaito mai magana da yawun Bataliya ta 12 Laftanar Hassan Abdullahi na cewa lamarin ya faru tun ranar 5 ga watan Satumba a Tunga.

Ya ƙara da cewa mutumin shi ne mataimakin Kachala Shuaibu, shugaban wani gungu da ke yawan kai hare-hare a Masalaci Boka da Dajin Ofere na jihar ta Kogi.

A cewarsa, daga baya kuma sun yi wa wani mai kai wa ‘yanfashin kayayyaki kwanton ɓauna a gadar Agbede–Adankoo, inda suka ƙwace makamai da kayayyaki.

Daga cikin abubuwan da suka samu a hannun ‘yanbindigar akwai harsasai, da wayoyin salula 31, da ƙunshin ƙwayoyi, da layu, da tsabar kuɗi N16,000.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *