Shugabannin PDP na jihohi sun marawa Damagum baya, tare da watsi da Abdurahman

0
1000271776
Spread the love

Kungiyar Shugabannin Jam’iyyar PDP ta Jihohi ta bayyana goyon bayanta ga Shugaban Jam’iyyar na Kasa, Umar Damagum.

Shugabannin sun sake jaddada goyon bayansu a wata sanarwa da suka fitar a wani taro inda suka yi watsi da bangaren da Abdulrahman Mohammed ke jagoranta a matsayin haramtaccen shugaba.

Taron, wanda ya kunshi shugabannin jihohi 29, ya ce Damagum ne kadai shugaban jam’iyyar da aka amince da shi a kasa a karkashin Kundin Tsarin Mulkin PDP (2017).

Shugabannin Jam’iyyar a cikin sanarwar sun ce, “Taron ya raba kansa da shugabancin Abdurahman kuma yana son ya ce PDP tana da Shugaba daya tilo, Mai Girma Umar Damagun.”

Ta yaba da abin da ta kira shugabancin hadin gwiwa tsakanin Kwamitin Aiki na Kasa, NWC, Kungiyar Gwamnonin PDP karkashin jagorancin Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, da kuma Hukumar Amintattu, BoT, wanda Adolphus Wabara ke jagoranta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *