Shugabannin duniya sun bayyana kisan Kirk a matsayin barazana ga dimukuraɗiyya

0
1000151464
Spread the love

Shugabannin duniya sun bayyana kisan jagoran matasa masu tsattsauran ra’ayi dake goyon bayan Trump, Charlie Kirk a Amurka a matsayin barazana ga Dimokraɗiyya, tare da yin gargaɗi kan irin illar da rikicin siyasa ke dashi.

Charlie Kirk mai shekaru 31, guda daga cikin matasa masu faɗa aji waɗanda ke goyon bayan Trump a siyasarsu ta masu tsattsauran ra’ayi, ya mutu bayan harbe shi da aka yi har lahira lokacin da yake jawabi yayin wani taro a jami’ar Utah Valley dake ƙasar Amurka a daren larabar nan.

A jawabinsa ga ‘yan ƙasa cikin wani faifan bidiyo da aka fitar a shafukansa na sada zumunta, Shugaba Donald Trump ya ce wannan lokaci ne na baƙin ciki ga Amurkawa, kuma yasha alwashin kamawa da hukunta duk waɗanda ke da hannu a kisan Charlie.

Shi ma Firaministan Canada Mark Carney ya bayyana kaɗuwarsa kan kisan Kirk, har ma ya ce babu wani gurbi na rikicin siyasa wanda ke barazana ga dimokraɗiyya a Amurka.

A nasa ɓangaren , Firaminista Keir Starmer na Birtaniya ya ce dole ne kowa ya samu damar faɗin albarkacin bakinsa ba tare da tsoro ko fargaba ba, yayin da twakwararsa ta Italiya, Giorgia Meloni ke cewa kisan Kirk mummanar illa ne ga dimokraɗiyya.

Shi kuwa Fira Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu wanda ya bayyana Kirk a matsayin babban aboki ga ƙasarsa, cewa ya yi an kashe shi ne saboda yana faɗin gaskiya, a dai-dai lokacin da kuma yake shirin kai masa ziyara a ƙasar ta Yahudu, bayan gayyatar da ya miƙa masa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *