Shugaban ‘Yan Bindiga Ado Aleru ya kashe mayakan sa guda 7 a Zamfara bisa zargin cin amana

0
1000116142
Spread the love

Shahararren shugaban ‘yan bindiga, Ado Aleru, ya kashe mayakan sa guda bakwai a wasu sassan jihar Zamfara, sakamakon zargin cin amana.

Wani mai sharhi a fannin tsaro Zagazola Makama ya bayyana cewa kashe-kashen ya faru ne a kauyukan Takulawa, Turba, Bamamu da kuma dajin Yamma.

A cewar majiyoyi, Aleru ya zargi mayakan sa da yin garkuwa da mutane ba tare da izini ba a kan hanyar Gusau zuwa Yankara, lamarin da ya ke ganin barazana ce ga ikonsa da ayyukansa.

Daya daga cikin majiyar ta ce “Ya kashe bakwai daga cikinsu bayan ya tabbatar da cewa suna da hannu a sace matafiya a kan babbar hanya kwanan nan.

Rahotanni sun ce kashe-kashen ya haifar da fargaba da rashin jin dadi a tsakanin sauran masu biyayya ga Aleru, wadanda ke ganin hukuncin kisa alama ce ta rashin yarda da juna a sansanin.

Aleru, wanda a baya gwamnatin tarayya ta ayyana shi a matsayin dan ta’addan da gwamnatin tarayya ke nema ruwa a jallo, an dade ana zarginsa da shirya sace-sacen mutane, kashe-kashe, da satar shanu a fadin jihohin Zamfara, Katsina da wasu sassan jihar Sakkwato.

Shugaban na ‘yan fashin ya kuma tattauna kan zaman lafiya da kwamitin tarayya domin kawo karshen tashe-tashen hankula a yankin Arewa maso Yamma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *