Shugaban Syria jajirtacce ne da zai iya ciyar da ƙasar gaba – Trump

Amurka ta ce Syria za ta shiga cikin kawancen da take jagoranta na yaki da mayakan IS, kuma za ta dawo da huldar diflomasiya da Washington.
Wakilin BBC ya ce bayan ganawar, Donald Trump ya bayyana shugaban na Syria a matsayin jajirtaccen mutum.
Shugaba Trump ya ce ya so Syria ta kasance wani babban bangare na shirinsa na samar da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya Kasa da shekara guda ne.
Ahmed Al Sharaa ya jagoranci mayaka suka kwace mulki a Damascus inda suka hambarar da gwamnatin Assad.
A wata hira da kafar Fox, Mr Sharaa ya ce tsohon mukaminsa na kwamandan al-Qaeda wani lamari ne da ya wuce.
