Shugaban mulkin sojin Niger na ziyarar aiki a yankin Tilaberi

Shugaban sojin Nijar, Janar Abdourahamane Tchiani ya kai ziyarar kwanaki biyu a jihar Tillabery, wurin da hare-haren ƙungiyoyin masu da’awar jihadi ya daidaita.
Shugaban ya samu rakiyar wata babbar tawaga da suka haɗa da ƙaramin ministan ƙasar kuma ministan tsaron ƙasar Salifou Mody, da babban hafsan hafsoshin soji, Moussa Salao Barmou, da sauran membobin gwamnati da na majalisar CNSP da wasu shuwagabanin hukumomi da ma’aikatu na gwamnati.
A yayin ziyararsa, shugaban ya ziyarci dakarun tsaron ƙasar da ke aikin tsaron ƙasar da al’umma wani matakin da yan ƙasar suka yaba da shi.
Hakazalika, shugaban ya yi muhimman jawaban da suka shafi tsaro da hadin kan al’umma da kuma matsin lambar da ƙasarsa ke fuskanta.
