Shugaba Tinubu ya isa Yola bikin ƙaddamar da ayyuka

0
1000544073
Spread the love

Shugaban kasa Bola Tinubu ya ziyarci jihar Adamawa a yau Litinin domin kaddamar da sabbin ayyukan da gwamnan Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri ya yi a Yola babban birnin jahar.

Daga cikin ayyuka da zai kaddamar sun hada da sabon ofishin gwamna da kofar shiga gidan gwamantin jahar da makarantar Model School, da titin Underpass da kuma dakin taro na babban kotun tarayya.

Akalla gwamnoni shida ne suka shigo Yola domin tabar shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, saboda kaddamar da ayyukan da gwamnatin Fintiri ta aiwatar.

Shugaban Bola ya yabawa Ahmadu Umaru Fintiri kan namijin kokari da ya yi a jahar sa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *