Shettima ya karɓi gwamnan Taraba a APC

Mataimakin Shugaban Najeriya, Kashim Shetiima ya wakilci Shugaban ƙasar Bola Tinubu wajen karɓar gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas da magoya bayansa zuwa jam’iyyar APC a hukumance.
An gudana da bikin karɓar gwamnan ranar Asabar a birnin Jalingo fadar gwamnatin jihar.
Yayin da yake jawabi a wurin taron, mataimakin shugaban ƙasar ya ce jihar Taraba da ɗaya daga cikin jihohi mafiya muhimmanci a fanni samar da abinci da makamashi da kuma tsaro ga Najeriya.
Shettima ya ce Shugaba Tinubu na sanar wa gwamnan cewa yana da matsayi ba iya a cikin jam’iyyar APC ba, har fannin ciyar da jihar gaba.
A ƙarshen shekarar da ta gabata ne gwamnan na Taraba ya sanar da komawarsa jam’iyyar APC bayan ficewa daga PDP tare da duka kwamishinoninsa.
