SDP ta rusa shugabancin Jihar Adamawa, tare da nada kwamitin riko na kwanaki 90

Kwamitin ayyuka na kasa na jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) ya sanar da rusa kwamitin ayyuka na jihar Adamawa, inda ya maye gurbinsa da kwamitin rikon kwarya na kwanaki 90 domin kula da harkokin jam’iyyar a jihar.
A wata sanarwa dauke da sa hannun sakataren jam’iyyar na kasa, Dr. Olu Agunloye, NWC, ta ce matakin ya biyo bayan nazari mai zurfi na ci gaba da aka samu a jihar Adamawa.
A cewar sanarwar, sabon kwamitin riko na da alhakin sake tsara tsarin jam’iyyar, da tara sabbin mambobin jam’iyyar, da kuma tabbatar da gudanar da ayyukan jam’iyyar yadda ya kamata domin tunkarar zabe mai zuwa.
Ana kuma sa ran kwamitin zai mika rahoton ci gaban da aka samu a kowane wata ga mataimakin shugaban shiyyar Arewa maso Gabas da kuma shugaban Jam’iyyar na kasa.
Daga cikin sauyin da akayi Shugaban kwamitin riko shi ne Paul Ahundana, wanda zai zama shugaban riko na jihar, Mohammed Abdulrahman ya zama sakataren riko na jihar.
Sauran manyan mambobin kwamitin sun hada da Hon. Salihu Aliyu (Mataimakin Shugaban Jam’iyyar), Dr. Zion Maina (Sakataren tsare tsare), Alhaji Saidu Mohammed (Ma’aji), da Misis Malia Sanweri (Sakatar Kudi), da dai sauransu.
Dokta Agunloye ya taya wadanda aka nada murna, sannan ya bukace su da su yi nazari sosai kan kundin tsarin mulkin jam’iyyar tare da kiyaye muhimman ka’idojin shugabanci na gari da adalci, wanda ya bayyana a matsayin ginshikin jam’iyyar SDP.
