Sabuwar taƙaddama ta ɓarke tsakanin Dangote da NUPENG

Sabuwar takaddama ta sake ɓarkewa tsakanin Dangote da ƙungiyar ƙwadago ta ma’aikatan dakon man fetur da iskar gas a Najeriya, NUPENG bayan kusan sa’o’i 48 da hukmar tsaron farin kaya ta DSS ta shiga tsakani wajen sulhunta su kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Shugabannin ƙungiyar sun dakatar da ɗibar mai a tashar matatar Dangote ranar Alhamis, bayan kamfanin ya bayar da umarni ga direbobi su cire dukkan sitikar ƙungiyar da aka liƙa a kan motocinsu a ranar Laraba.
Daily Trust ta ruwaito cewa DSS ta shiga tsakani ranar Talata, bayan taron sulhu na farko da aka yi ranar Litinin ya ƙare ba tare da cimma matsaya ba kan batun ƙungiyoyi.
Amma kuma bayan taron sirri da aka gudanar a hedkwatar DSS a Abuja, shugabannin NUPENG sun umarci membobinsu da su janye yajin aikin da suke yi baki ɗaya.
