Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta sake samun wani nasaran kama 6arawon Motoci

Jami’an rundunar ‘yan sandan Jahar Adamawa da ke karkashin DPO Yola Division sun gudanar da binciken kwakwaf tare da kama wani mai suna Musa Suleh ‘Dan garin Uba, karamar hukumar Hong bisa mallakar wasu motoci da ake zargin na sata ne.
An kama wanda ake zargin ne a tashar mota ta Jambutu, karamar hukumar Yola ta Arewa inda bayan da aka yi masa tambayoyi, ya amsa laifin satar wata mota kirar Toyota Starlet, mai lamba YLA-420 mallakar wani Mai suna Babawo Abubakar na garin Ngurore, karamar hukumar Yola ta Kudu.
A yayin binciken an kuma gano wani Motar Toyota Starlet, mai lamba JAL-861 CL an same shi a hannunsa ba tare da ko wata takarda ko shaidar mallakar abin da ke tabbatar da mallakar motar ba.
Rundunar ‘yan sandan ta yi kira ga jama’a da su baiwa ‘yan sanda hadin kai ta hanyar bayar da bayanai kan lokaci kuma masu amfani dangane da munanan dabi’u a kusa da su da kuma tabbatar da jajircewar rundunar na kare rayuka da dukiyoyi.
Kawo yanzu dai rundunar zata gurfanar da wanda ake zargin zuwa kotu bayan kammala bincike.
