Rundunar sojin Najeriya ta ce ta yaye ƙarin kurata 3,439

0
1000367657
Spread the love

Hafsan sojin ƙasa na Najeriya, Laftanar Janar Waidi Shaibu (NAM), ya yi kira ga sabbin jami’an soja 3,439 da aka horas da su dukufa wurin nuna ƙwarewa yayin gudanar da ayyukansu.

Dakarun da aka ɗauka waɗanda ke cikin runduna ta 89 na rundunar sojojin Najeriya, sun samu nasarar kammala horon na tsawon watanni shida a Nigerian Army Depot da ke Zariya.

Yayin bikin yaye sojojin, Laftanar Janar Shaibu ya ce horon da aka ba su zai tabbatar da cewa sun yi aiki tuƙuru cikin jajrcewa da nuna kisshin ƙasa.

Ya tunatar da su kan irin rantsuwar da suka yi, yana mai cewa: “Da wannan rantsuwar, yanzu ya zama dole ku bi dokokin farar hula da na soja, ku guje wa duk wani abu da zai ɓata sunan sojojin Nijeriya ko kuma ƙasa, ku yi hidima da mutunci, da aminci da kuma biyayya ga hukuma.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *