Rikici ya sake ɓarkewa tsakanin dakarun gwamnati da M23 a DR Congo

An ci gaba da gwabza faɗa a gabashin Jamhuriyyar Demokraɗiyya Congo duk da rattaɓa hannu a yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin wakilcin gwamnatin ƙasar dana ƙungiyoyin M23 da AFC yayin bikin da ya gudana a ranar 15 ga watan nan a Doha.
Tun da asubahin jiya Litinin aka faro faɗan tsakanin ɓangaren mayaƙan da dakarun gwamnati a dukkanin yankunan arewaci da kuma kudanin Kivu kwanaki 2 tal bayan rattaɓa hannu kan yarjejeniyar ta birnin Doha da Qatar ta jagoranta, wadda dukkanin ɓangarorin suka amince da tsagaita wuta.
Rikicin na baya-bayan nan ya nuna cewa a takarda ne kaɗai ɓangarorin biyu ke mutuntawa koma suka aminta da wannan yarjejeniya.
Wasu majiyoyi sun shaidawa kafar RFI sashen Faransanci cewa tun daga tazarar kilomita 30 daga birnin Bukavu ake jiyo sautin musayar wutar ɓangarorin biyu, wwanda bayanai ke cewa mayaƙan ƙungiyoyin na AFC da M23 sun riƙa fitowa daga ƙauyen Civanga na gandun dajin Kahuzi-Biega wanda dama mayaƙan ƙungiyoyin biyu ne ke iko da shi.
