Rashin tsaro na neman fin ƙarfin gwamnatin Najeriya – Kwankwaso

Jagoran jam’iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, ya nuna matuƙar damuwa kan yadda matsalar tsaro ke ta ’kara munana a Najeriya, yana mai gargaɗin cewa matsalolin tsaro da ke faruwa yanzu na neman ya fi ƙarfin gwamnati.
Ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X.
Kwankwaso, wanda ya taɓa zama gwamnan Kano, ya ce alamu na nuna cewa matsalolin tsaro da ke faruwa yanzu ka iya zama babbar barazana ga haɗin kai da kwanciyar hankalin ƙasa.
