Rashin kwarewa da iya mulki yasa har yanzu ba’a nada jakadu ba – Tambuwal ya caccaki Tinubu

Sanatan Sokoto ta Kudu, Aminu Tambuwal, ya bayyana cewa shugaban kasa Bola Tinubu bai da ilimin yadda zai tafiyar da mulkin Najeriya shi ya sa ya kasa nada jakadu har yanzu.
Tsohon gwamnan jihar Sokoto ya bayyana hakan ne a lokacin da yake amsa tambayoyi a Gidan Talabijin na Channels.
A cewar Tambuwal: “Tinubu a kodayaushe yana killace a yankinsa a cikin Legas, bai fahimci tsarin tarayya ba, har ya zuwa yanzu, ba mu da jakadu.
“Shekaru biyu da kusan watanni uku a kan mulki me hakan ya gaya maka, Tinubu bai da ilimin Najeriya a matsayin kasa.
