PDP ta ɗage taron kwamitin zartarwarta karo na 103

Babbar jam’iyyar hamayya ta PDP a Najeriya ta ɗage babban taron kwamitin zartarwarta da aka tsara yi ranar Laraba 15 ga watan Oktoban 2025.
Cikin wata sanarwar da jam’iyyar ta wallafa a shafinta na X, ta ce ta ɗauki matakin ne a taron gaggawa da kwamitin gudanarwar jam’iyyar ya yi a Abuja ranar Litinin.
Jam’iyyar ta ce ta ɗage taron zuwa wani lokaci da za ta sanar a nan gaba, don haka ta buƙaci mambobinta su jira sanarwa ta gaba game da sabuwar ranar taron.
Jam’iyyar PDP dai na fuskantar matsin lamba, sakamakon yawan ficewar mambobinta zuwa APC mai mulki.Ko a baya-bayan nan ma an yi ta raɗe-raɗin ficewar wasu gwamnoninta biyu zuwa APC mai mulki.
