Pakistan da Afghanistan na rikici kan iyakan ƙasa

0
1000228549
Spread the love

Rikici ya sake ɓarkewa tsakanin ƙasashen Pakistan da Afghanistan sa’o’i ƙalilan kafin ƙarewar wa’adin yarjejeniyar tsagiata wuta ta kwanaki biyu da suka cimma.

Ƙasashen Pakistan da Afghanistan sun shafe shekaru suna gwabza rikicin kan iyaka tsakaninsu, wanda ya kashe gwamman mutane, kuma ya tilasta kwashe mutane daga muhallansu.

Yarjejeniyar zaman lafiyar wadda ta fara aiki da ƙarfe 1 agogon GMT a ranar larabar nan za ta ƙare ne a ranar Juma’ar nan da ƙarfe 1 agogon GMT, a wani yanayi da dukkan ɓangarorin biyu ke iƙirarin cewa bashi ne ya buƙaci a tsagaita wutar ba.

Ƙasar Pakistan wadda ta tabbatar da fara aikin yarjejeniyar, ta ce hakan zai bai wa ƙasashen biyu damar lalubo hanyar masalaha game da rikicin nasu, yayin da a ɓangarenta gwamnatin Taliban ta umarci dakarunta su mutunta yarjejeniyar.

To sai dai tuni suka fara kaiwa juna hare-hare gabanin ƙarewar wa’adin yarjejeniyar zaman lafiyar da aka cimma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *