NNPC ya sanar da samun ribar fiye da naira tiriliyan 5 cikin shekarar 2024

Kamfanin mai na Najeriya NNPC ya sanar da samun ribar naira tiriliyan 5 da biliyan 400 bayan cire haraji, da kuma kuɗaɗen shiga na naira tiriliyan 45 da biliyan 100 a shekarar 2024 da ta gabata.
Wannan na ƙunshe ne cikin sanarwar da kamfanin ya fitar a yau Litinin, ɗauke da sa hannun daraktan yaɗa labaran NNPC, Andry Odeh.
Sanarwar ta ce NNPC na shirin ƙara yawan mai da iskar gas ɗin da yake samarwa, kana yana sa ran samun kuɗaɗen shiga na Dala biliyan 60 nan da shekarar 2030.
Shugaban NNPC, Bashir Bayo Ojulari, ya ce wannan ci gaban da suke samu na nuni da irin tasirin ayyukansa da sauye-sauye da gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta yi, don haɓaka tattalin arziƙin Najeriya.
Ojulari ya sake jaddada aniyarsa ta ci gaba da jajircewa wajen ƙaddamar da ayyukan da za su haɓaka tattalin arziƙin ƙasar, baya ga sauƙaƙawa al’umma.
