NEMA ta gargaɗi mazauna kusa da Kogin Neja su yi hijira

0
1000088718
Spread the love

Hukumar ba da agajin gaggawa a Najeriya, NEMA ta gargaɗi mazauna kusa da Kogin Neja da su tashi saboda ƙaruwar yawan ruwan kogin.

Shugabar hukumar, Zainab Umar, ta umarci ofisoshinta da ke kusa da kogin da su ɗaura ɗamarar wayar da kan mazauna jihohin Kebbi da Neja da Kwara, waɗanda ke maƙwabtaka da ƙasar Benin.

Wata sanarwa da hukumar ta fitar ta nemi mazauna jihohin da su koma wurare masu tudu domin guje wa ambaliyar da ka antayowa.

Sai dai Nema ba ta faɗi wani takamaiman lokaci da take hasashen faruwar hakan ba

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *