NDLEA ta kama manyan ‘yan daba guda tara, ta kama ɗimbin miyagun ƙwayoyi a faɗin Nigeria

Hukumar dake yaki da miyagun kwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) ta ƙarfafa ayyukanta na yaƙi da miyagun ƙwayoyi a faɗin Nigeria, inda ta wargaza manyan ƙungiyoyi shida, ta kama waɗanda ake zargi da aikata manyan laifuka guda tara, sannan ta kwace muggan ƙwayoyi masu yawa tsakanin 17 da 22 ga Nuwamba, 2025.
Ayyukan sun shafi filayen jirgin sama, manyan hanyoyi, rumbunan ajiya, kasuwanni, da dandamali na kan layi.
A filin jirgin saman Murtala Muhammed International, Lagos, jami’an tsaro sun kama muggan ƙwayoyi da aka ɓoye a cikin silinda na’urorin matsa lamba da aka shigo da su daga Afirka ta Kudu.
An kama mutane biyu da ake zargi, Ebulue Lotanwa Uzochukwu da Christopher Michael Ndibuisi, yayin da suke ƙoƙarin tattara kwayoyi na methamphetamine, Loud, cocaine, da sauran abubuwa.
