NDE ta horar da matasa marasa aikin yi 400, kan harkokin noma a Adamawa

0
1000049214
Spread the love

Hukumar Kula da samar da Aiki ta Kasa (NDE) ta horar da marasa aikin yi 400 kan harkokin noma a jihar Adamawa da nufin samar da damarmakin aiki da kuma tabbatar da dogaro da kai ga harkokin kasuwanci.

Jami’ar Yada Labarai ta Hukumar, Hajiya Aisha Madu Fika ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Laraba a Yola, inda ta nuna cewa an samar da kayayyakin aiki ga wadanda suka ci gajiyar su 400, ciki har da matasa da mata, a fannoni shida (6) daban-daban na harkokin noma kamar su tsarin horar da manoma mai dorewa, tsarin horar da manoma kanana da kuma tsarin horar da kiwon awaki.

Sanarwar ta kuma ambaci wasu fannoni na horon da suka hada da; tsarin horar da samar da kifi, tsarin horar da manoma kan harkokin noma a cikin al’umma da kuma tsarin horar da manoma kan halittu.

Fika ta bayyana cewa, horon yana tsakanin watanni daya zuwa uku bi da bi, kuma Hukumar tana aiki kan yadda za ta karfafa wa wadanda aka yaba da kuma wadanda aka dage a kansu su fara kasuwancinsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *