NCC ta fadada wayar da kan jama’a game da illolin satar fasaha ga makarantu da masu sayar da littattafai a Adamawa

A ci gaba da aikin wayar da kan jama’a na shekara-shekara kan illolin satan fasaha ta haramtacciyar hanya, Hukumar kula da Haƙƙin mallaka ta Najeriya, NCC ta fara kamfen a makarantu masu zaman kansu da kamfanonin buga littattafai a jihar Adamawa.
Mai riƙon ƙwarya na Hukumar, NCC, Yusuf Ibrahim ya bayyana wa masu mallakar makarantu masu zaman kansu da jami’an zartarwa na ayyukan kampunan buga littattafai da suka ziyarta a Yola ranar Litinin cewa, Hukumar ta himmatu wajen tabbatar da kare haƙƙin mallakar littattafai.
Ibrahim ya gargaɗi masu sayar da littattafai da su yi taka-tsantsan da shiga cikin harkokin da suka shafi satar fasaha, yana mai gargadin cewa dokar NCC ta sanya takunkumi mai tsauri ga waɗanda suka ƙi bin ƙa’ida, musamman waɗanda ke cikin masana’antar da ake gudanar da ayyukan buga littattafai.
A lokacin tattaunawa da masu mallakar littattafai da shugabannin buga littattafai a ofisoshinsu, ƙungiyar NCC ta duba littattafan karatu, takardun kuɗi da rasit da ke ɗauke da cikakkun bayanai game da tushen littattafan da ke hannunsu don tantancewa.
Da yake mayar da martani ga ziyarar, Ma-mallaka Makarantun Kim Standard Foundation, Misis Elizabeth Abraham Durosimi da Kwalejin Bishaq Global Academy Yola, Aisha Hajja Rilwanu, sun yaba da kokarin NCC, suna mai jaddada cewa zai taimaka sosai wajen kare kadarorin marubutan littattafan da aka buga.
A cikin martani daban-daban da suka bayar a lokacin ziyarar a harabar kasuwancinsu, masu kula da shagunan Valla Printing Enterprise Yola da Alvaris Communities Ltd.Mr.Nuhu Yohanna da Mista Albert Mark Asachaya sun ce NCC tana yin “babban aiki” wajen sauƙaƙa kasuwancinsu tare da kamfen ɗin wayar da kan jama’a da jama’a ke matuƙar buƙata.
Rahotanni sun bayyana cewa makarantu masu zaman kansu da aka ziyarta sun haɗa da Makarantar Kim Standard Foundation School Yola, Kay Academy Yola, Naxora Academy Yola, Play and learn School da kuma Bishaq’s Global Academy Yola.
Sauran ziyarar wuraren kasuwanci da tawagar NCC ta kai sun haɗa da; Valla Printing Enterprise da Alvaris Communication Ltd.Yola bi da bi.
