Najeriya na fuskantar haɗarin faɗawa mulkin kama-karya – Atiku

0
20250601_134212
Spread the love

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya ce hare-haren da aka kai kan masu gudanar da taro a jihohin Kaduna da Katsina da Kebbi a matsayin abubuwan da ke da haɗarin “jefa Najeriya cikin tsarin kama-karya a ƙarƙashin gwamnatin Bola Tinubu.”

A ƙarshen makon da ya gabata ne wasu da ba a san ko su wane ne ba suka kai hari tare da tayar da tarzoma a wani wurin taron ƴaƴan jam’iyyar hadaka ta ADC a birnin Kaduna.

Cikin mahalarta taron har da jiga-jigan jam’iyyar ta ADC, tsohon gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai da kuma shugaban jam’iyyar na Arewa maso yamma.

Daga baya, a jiya Alhamis rundunar ƴansandan Najeriya a jihar ta Kaduna ta aika da takardar gayyata ga jam’iyyar ta ADC da kuma jagororinta da su bayyana a gabanta domin bayar da bahasi kan hatsaniyar da aka samu a lokacin taron.

A cikin wata sanarwa da tsohon ɗan takarar shugabancin Najeriyar ya fitar a shafinsa na X, Atiku ya ce “gayyatar da aka yi wa Nasir El-Rufai da harin da aka kai kan tawagar tsohon ministan shari’a na Najeriya Abubakar Malami da kuma tarwatsa taro kan matsalar tsaro na ƙungiyar dattijan Katsina” a matsayin abin damuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *