NAFDAC ta haramta amfani da abincin yara na Bledine

Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna a Najeriya (NAFDAC) ta gargaɗi ƴan kasar su kaucewa amfani da wani abincin yara mai suna Bledine, bayan rahotanni cewa ƙasar Chadi ta haramta abincin saboda fargabar gurɓacewa.
A cikin wata sanarwa a shafinta na X, NAFDAC ta ce wani kamfanin Faransa mai suna Danone ne ke haɗa abincin, kuma sun haɗa da mai haɗin biskit da madara da ayaba.
A cewar ta, bisa rahotanni da ta samu, hukumomi a Chadi sun haramta amfani da abincin yaran bayan ya gaza cika ƙaidojin da aka sanya ba kan sinadarin Aflatoxin B1, wani sinadari da hukumar ta ce na da illa ga ƙananan yara.
Hukumar ta ce tuni wannan abinci ya soma yawo a kasuwanni a faɗin Najeriya, musamman a garuruwan da ke kusa da iyakokin ƙasar da Chadi.
NAFDAC ta ce ta umurci Jami’anta da ke kowane shiyya ta kasar, da na matakin jihohi su soma bincikar kasuwanni tare da ƙwace abincin yaran.
