Na yi tunanin Buhari zai magance matsalar Boko Haram – Jonathan

0
1000200337
Spread the love

Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya ce ƙungiyar Boko Haram ta taɓa zaɓar tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a matsayin mai shiga tsakani domin tattaunawa da gwamnatin tarayya a zamanin mulkinsa.

Jonathan ya bayyana haka ne a ranar Juma’a a wajen ƙaddamar da littafin “Scars: Nigeria’s Journey and the Boko Haram Conundrum“, wanda tsohon babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Lucky Irabor ya rubuta a Abuja.

Ya ce, a lokacin an fara yunƙurin tattaunawa ne da Boko Haram domin ganin ko za a samu sulhu, su daina yaƙin da suke yi.

“An kafa kwamiti ne a lokacin, sai Boko Haram ta zaɓi Buhari a matsayin wakilinsu domin tattaunawa da gwamnatin,” in ji Jonathan kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Jonathan ya ce, “tunda dai har suka zaɓe shi a matsayin wakili, to sai na yi tunanin da zarar ya hau mulki, zai kawo ƙarshen matsalar, amma abin mamaki har yanzu ana fama da matsalar ta Boko Haram.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *