Mutum daya ya mutu, wasu jami’ai sun samu raunuka yayin da wasu ’yan daba suka kai hari ofishin ‘yan sandan Kano

Akalla mutum daya ne aka tabbatar da mutuwarsa yayin da wasu kuma suka samu raunuka daban-daban biyo bayan wani harin da wasu ‘yan ta’adda suka kai ofishin ‘yan sanda na Garko a jihar Kano.
Wata sanarwa da kakakin rundunar ƴan sandan Jihar ya fitar a ranar Asabar ta bayyana cewa ‘yan ta’addan sun kai hari ofishin ne a lokacin da suke nuna rashin amincewarsu da mutuwar wani mazaunin unguwar Wudil, wanda ake zargin wasu mutane uku ne suka kashe shi.
A cewar sanarwar, a ranar Juma’a 5 ga watan Satumba, 2025, jami’an rundunar ‘yan sandan yankin Wudil sun kama wasu mutane uku da ake zargi da hannu a kisan tare da kai su sashin ‘yan sanda na Garko domin ci gaba da bincike.
Sanarwar ta bayyana cewa, a yayin da ake ci gaba da yi wa wadanda ake zargin tambayoyi, wani taron matasa dauke da sanduna da duwatsu, da ke nuna fushi da mutuwar wanda aka kashe, sun kai hari ga sashen, inda suka hargitsa ayyukan ‘yan sanda da nufin murkushe wadanda ake zargin.
Ya ce wannan aika-aikar ya janyo hasarar dukiya mai dimbin yawa da suka hada da kona wata motar sintiri ta sashen, da lalata motoci uku na hukumar Hisbah na karamar hukumar Garko, da fasa gilasan ginin ofishin ‘yan sanda.
