Mutanen da suka mutu sakamakon zaftarewar kasa a Sudan ya kai 1000

0
1000110128
Spread the love

Aƙalla mutum dubu guda aka tabbatar da mutuwar su a zaftarewar ƙasar da ta afku a yankin Darfour da ke yammacin Sudan,bkamar yadda watabƙungiya mai fafutukar kare al’umma a yankin ta sanar a wanan talata.

A cewar ƙungiyar iftila’in ya afkawa ƙauyen Tarasin na lardin Darfour ne inda ake fargabar dukkan mazauna kauyen sun rasa rayukansu.

Gwamnan lardin Darfour Minni Arko Minawi, ya bayyana lamarin da mafi muni da aka taɓa gani.

A wani sako da ta wallafa, ƙungiyar da ke gwagwarmaya kare muradun al’umma yankin ta kira Majalisa Dinkin Duniya da ƙungiyoyin jinkai da su kawo dauki domin ceto dimbin mutanen da suka maƙale.

Tun bayan da Sudan ta tsunduma yakin basasa a shekara 2023, galibin yankunan musamman a yammacin ƙasar suka fada karkashin ikon ƙungiyoyi masu dauke da makamai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *