Mutane uku sun mutu, bakwai sun jikkata, tare da kone gidaje a rikicin kabilanci a Jigawa

0
1000219044
Spread the love

Rundunar ‘yan sanda a jihar Jigawa ta tabbatar da kashe mutane uku yayin da bakwai suka samu munanan raunuka a wani rikicin kabilanci da ya barke a karamar hukumar Birniwa.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, SP Lawan Shiisu Adam, ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin.

Ya ce lamarin ya faru ne a ranar Laraba da daddare inda wasu da ake zargin masu aikata laifuka ne suka kai farmaki kauyen Dagaceri, inda suka kona gidaje tare da kai wa mutane hari.

Ya ce, rundunar hadin guiwa ta jami’an tsaro ta hanzarta zuwa wurin domin dawo da zaman lafiya tare da cafke mutane bakwai da ake zargi da hannu a rikicin.

SP Shiisu ya kara da cewa jami’an tsaro sun kwato wayoyin hannu da laya a wurin da harin ya faru.

Ya ce ana ci gaba da bincike don gano musabbabin harin.

Ya yi kira ga mazauna yankin da su himmatu wajen samar da ingantaccen tsarin aikin ‘yan sanda da na gargadin gaggawa don hana ci gaba da zubar da jini.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *