Muna neman maganin dafin maciji don rage mace-macen cizon maciji – ACPN

Ƙungiyar Masana Magunguna ta Najeriya ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta samar da maganin dafin maciji da ba shi da illa ga lafiya a duk faɗin ƙasar.
Ƙungiyar ta kuma yi kira ga masana’antar magungunan dafin da ke cikin gida da ta magance mace-mace sama da 2,000 dake da alaka cizon maciji da ake samu a kowace shekara.
Kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya ya ruwaito a ranar Talata, ACPN ta yi roƙon ne a cikin wata sanarwa da Shugaban Ƙungiyar ta na Ƙasa, Ambrose Eze ya fitar.
Ya yi gargaɗin cewa cizon maciji ya kasance ɗaya daga cikin matsala na gaggawa na lafiyar jama’a da aka fi watsi da shi a Najeriya, wanda ke buƙatar kulawar gaggawa ta ƙasa.
Ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta ayyana cizon maciji a matsayin batu na fifiko ga Lafiyar Ƙasa kuma ta sanya shi a matsayin Cutar da za’a kula da Ita.
Ya lura cewa magungunan kashe dafin har yanzu suna cikin jerin magungunan da ake bukata, duk da haka mace-macen da suka shafi cizon maciji na ci gaba da karuwa.
